
Karanta ko saurari wannan sakin layi mai zuwa
Roƙon mahaifiya
20:20Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu.21Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?”
Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”
22Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?”
Suka amsa, “Za mu iya.”
23Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”
24Da goman suka ji haka, sai suka yi fushi da ’yan’uwan nan biyu. 25Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko. 26Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku, 27kuma duk mai son zama shugaba, dole yă zama bawanku, 28kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.
Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.
Get Discovery Bible Studies on your phone
Discover copyright ©2015-2026 discoverapp.org
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™. Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.. "Biblica" wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.