
Karanta ko saurari wannan sakin layi mai zuwa
Fāɗuwar mutum
3:1To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”2Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, 3amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”
4Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. 5Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”
6Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci. 7Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.
8Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu. 9Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
10Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”
11Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
12Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”
13Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
14Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka,
“Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji!16Sa’an nan ya ce wa macen,
“Zan tsananta naƙudarki ainun,17Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’
“Za a la’anta ƙasa saboda kai.20Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.
21 Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura. 22Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.” 23Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi. 24Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.
Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.
Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.
Get Discovery Bible Studies on your phone
Discover copyright ©2015-2026 discoverapp.org
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™. Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.. "Biblica" wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.