
Karanta ko saurari wannan sakin layi mai zuwa
Bikin Ƙetarewa
12:1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna a Masar, 2“Wannan wata za tă zama a gare ku wata na farko, wata na fari na shekararku. 3Ka faɗa wa dukan jama’ar Isra’ila cewa a rana ta goma ga wannan wata, kowane mutum zai ɗauki ɗan rago domin iyalinsa, ɗaya domin kowane gida. 4In akwai wani gidan da ba za su iya cinye rago guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki rago guda gwargwadon yawansu, bisa ga abin da mutum guda zai ci. 5Dabbobin da za ku zaɓa, dole su zama bana ɗaya, namiji marar tabo, za ku kuma kamo su daga cikin tumaki ko awaki. 6Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato, sa’ad da dukan taron jama’ar Isra’ila za su yanka ragunansu da yamma. 7Sa’an nan za su ɗauki jinin, su shafa a gefen da yake saman dogaran ƙofa na gidajen da suke cin naman dabbobin. 8A wannan dare, za su gasa naman, su ci da ganyaye masu ɗaci, da kuma burodi marar yisti. 9Kada ku ci nama ɗanye, ko kuma dafaffe, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kuma kayan cikin. 10Kada ku bar kome yă kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi. 11Ga yadda za ku ci shi, ku yi ɗamara, takalma kuwa a ƙafafunku, kuna riƙe da sandunan tafiya a hannunku. Ku ci shi da gaggawa; Bikin Ƙetarewa ne na Ubangiji.12“A wannan dare, zan ratsa Masar, in bugi kowane ɗan fari, na mutum da na dabba, zan kuma hukunta dukan gumakan Masar. Ni ne Ubangiji. 13Jinin zai zama alama a gare ku, a gidajen da kuke; sa’ad da kuwa na ga jinin, zan ƙetare ku. Ba wata annoba mai hallakarwa da za tă taɓa ku yayinda na bugi Masar.
14“Wannan rana za tă zama muku abin tunawa dukan zamananku masu zuwa, za ku kiyaye ta kamar biki ga Ubangiji, dawwammamiyar farilla ce har abada. 15Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti. A rana ta fari, za ku fid da yisti daga gidajenku gama duk wanda ya ci abu mai yisti daga rana ta fari har zuwa rana ta bakwai, za a fid da shi daga Isra’ila. 16A rana ta fari, za ku yi taro mai tsarki, haka kuma za ku sāke yi a rana ta bakwai. Kada ku yi aiki a waɗannan ranaku, sai dai ku shirya abinci domin kowa, abin da za ku yi ke nan kawai.
17“Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti domin a wannan rana ce na fitar da ku ɓangare-ɓangare daga Masar. Ku kiyaye wannan rana ta zama muku dawwammamiyar farilla wa tsara masu zuwa. 18A wata na fari, za ku ci burodi marar yisti daga yammancin ranar goma sha huɗu har zuwa yammancin ranar ashirin da ɗaya. 19Kada a sami yisti a gidajenku har kwana bakwai. Kuma duk wanda ya ci wani abu mai yisti, za a fid da shi daga taron jama’ar Isra’ila, ko baƙo ne, ko haifaffen ɗan ƙasa. 20Kada ku ci wani abincin da aka yi da yisti. Ko’ina kuka zauna, dole ku ci burodi marar yisti.”
21Sa’an nan Musa ya kira dukan dattawan Isra’ila ya ce musu, “Ku je da sauri ku zaɓi dabbobin iyalanku, ku yanka ragon Bikin Ƙetarewa. 22Ku ɗauki ƙunshin itacen hizzob, ku tsoma cikin jinin da yake a kwano, ku yayyafa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada wani daga cikinku yă fita daga ƙofar gidansa sai da safe. 23Sa’ad da Ubangiji yake ratsa ƙasar don yă bugi Masarawa, zai ga jinin a bisa da kuma gefen madogaran ƙofa, zai ƙetare ƙofar, ba zai bar mai hallakawa yă shiga gidajenku, yă buge ku ba.
24“Ku kiyaye waɗannan dokokin a matsayin dawwammamiyar farilla, da ku da ’ya’yanku har abada. 25Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku yadda ya alkawarta, ku kiyaye wannan biki. 26Sa’ad da kuma ’ya’yanku suka tambaye ku, ‘Mece ce manufar wannan biki?’ 27Sai ku faɗa musu, ‘Hadaya ce ta Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.’ ” Sai mutane suka rusuna, suka yi sujada. 28Isra’ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.
Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.
Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.
Get Discovery Bible Studies on your phone
Discover copyright ©2015-2026 discoverapp.org
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™. Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.. "Biblica" wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.