Gano

Nazari 2

Farashin Zama Mai Bi.

Luka 14:25-33

Mataki na 1: Karanta labarin

Karanta ko saurari wannan sakin layi mai zuwa

x1.0

Wahalar rayuwar almajiri

14:25Taron mutane mai yawa suna tafiya tare da Yesu, sai ya juya ya ce musu, 26“Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.

28 “In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin. 29Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa ba’a, 30yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’

31 “Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya ƙarawa da mai zuwa da dubu ashirin? 32In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama. 33Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.

Mataki na 2: Sake ba da labarin.

Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.

Mataki na 3: Gano Labarin

Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.


Get it on Google Play
Download on the App Store

Get Discovery Bible Studies on your phone

Discover copyright ©2015-2026 discoverapp.org

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™. Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.. "Biblica" wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.