
Karanta ko saurari wannan sakin layi mai zuwa
Yesu ya yi alkawarin Ruhu Mai Tsarki
14:15 “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina. 16Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, 17Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku. 18Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku. 19Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu. 20A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku. 21Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.
Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.
Get Discovery Bible Studies on your phone
Discover copyright ©2015-2026 discoverapp.org
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™. Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.. "Biblica" wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.