
Karanta ko saurari wannan sakin layi mai zuwa
Babban umarni
28:16Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. 17Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.
Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.
Get Discovery Bible Studies on your phone
Discover copyright ©2015-2026 discoverapp.org
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™. Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.. "Biblica" wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.