
Karanta ko saurari wannan sakin layi mai zuwa
23:32Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye. 33Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. 34Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.
35Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”
36Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami. 37Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”
38Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce,
Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.
39Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”
40Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi? 41Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”
42Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.”
43Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”
Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.
Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.
Get Discovery Bible Studies on your phone
Discover copyright ©2015-2026 discoverapp.org
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™. Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.. "Biblica" wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.