23:1
Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,
2Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,
yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,
3yakan maido da raina.
Yakan bi da ni a hanyoyin adalci
saboda sunansa.
4Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
5Ka shirya mini tebur
a gaban abokan gābana.
Ka shafe kaina da mai;
kwaf nawa ya cika har yana zuba.
6Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
Mataki na 2: Sake ba da labarin.
Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.
Mataki na 3: Gano Labarin
Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.
Me wannan labari ke gaya maka game da Allah?
Me wannan labari ke gaya maka game da mutane?
Idan wannan da gaske maganar Allah ce, wane canje-canje za ka yi a rayuwarka?