Gano

Nazari 12

Fansar: Annabcin Ishaya na bawan da ke shan wahala

Ishaya 53:1-12

Mataki na 1: Karanta labarin

Karanta ko saurari wannan sakin layi mai zuwa

x1.0
  53:1Wa ya gaskata saƙonmu
    kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?
  2Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi,
    kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa.
  Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu,
    babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa.
  3Mutane suka rena shi suka ƙi shi,
    mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala.
  Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi
    aka rena shi aka yi banza da shi.
  4Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
    ya kuma daure da baƙin cikinmu
  duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
    ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
  5Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,
    aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;
    hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,
    kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.
  6Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata,
    kowannenmu ya kama hanyarsa;
  Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa
    hukuncin da ya wajaba a kanmu.

  7Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba,
    duk da haka bai buɗe bakinsa ba;
  aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka,
    kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru,
    haka bai buɗe bakinsa ba.
  8Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi.
    Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa?
    Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai;
    saboda laifin mutanena aka kashe shi.
  9Aka yi jana’izarsa tare da mugaye,
    aka binne shi tare da masu arziki,
  ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba,
    ko a sami ƙarya a bakinsa.

  10Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala,
    kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi,
  zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai,
    nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.
  11Bayan wahalar ransa,
    zai ga hasken rai, ya kuma gamsu;
  ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa,
    zai kuma ɗauki laifofinsu.
  12Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya,
    zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi,
  domin ya ba da ransa har mutuwa,
    aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi.
  Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa,
    ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.

Mataki na 2: Sake ba da labarin.

Dauki 'yan lokuta ka sake ba da labarin a cikin kalamanka. Kana iya son faɗa shi a fili, ko rubuta shi. Idan ka ga kana wahala wajen tuna shi, karanta ko saurara shi sake.

Mataki na 3: Gano Labarin

Lokacin da ka ji cewa ka saba da labarin, ɗauki lokaci ka yi tunani ko tattauna tambayoyin masu zuwa.


Get it on Google Play
Download on the App Store

Get Discovery Bible Studies on your phone

Discover copyright ©2015-2026 discoverapp.org

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™. Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™. Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.. "Biblica" wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.